Ma’aikatar aikin gona da kare muhalli ta Lebanon tare da rundunar zaman lafiya ta MDD ( UNIFIL) sun yi aikin hadin gwiwa akan sanadarorin da jiragen Haramtacciyar Kasar Isra’ila su ka watsa a kudancin kasar, da hakan yake a matsayin keta tsagaita wutar yaki.
Bangarorin biyu sun kwashi kasa a yankunan da aka watsa sanadarorin domin gudanar da bincike da sanin tasirin da zai yi akan kasar noma da kuma lafiyar mazauna yankunan.
Sanadarin da sojojin “Isra’ila” su ka watsa a yankin sunanshi ( Glyphosate) wanda yake kashe tsire-tsire a yankin da aka watsa shi.
Ma’aikatar aikin gona da muhalli ta kasar Lebanon ta sanar da cewa, watsa wannan sanadarin da ya rubanta wanda ake zubawa a gona da rubanya har sau 20 zuwa 30, aiki ne yaki da wuce gona da iri. Haka nan kuma lamarin yana a matsayin barazana ga noma da samarwa kasa abinci.
Wani sashe na bayanin ya kunshi cewa, sanadarorin da Isra’ilan ta watsa a kudancin Lebanon, za su yi illa ga rayuwar manoma da kuma abinci da ruwan sha.
Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila dai ba su girmama tsagaita wutar yaki da kasar ta Lebanon da aka cimmawa a 2024,ta yadda kusan kowace rana suna kai hari.