Jaridar ‘al-Nahar’ ta kasar Lebanon ta dauki labarin rasuwar Sayyid Abdulkarim Nasrallah da shi ne mahafin Shahid Sayyid Hassan Nasrallah tsohon babban magatakardar kungiyar Hizbullah.
An yi jana’izar Abdulkarim Nasrallah ne a garin Gubair da ta sami halaryar dubban mutane da su ka hada shugabannin Hizbullah da kungiyar Amal da baki daga wasu bangarori na kasar ta Lebanon.
An haifi Nasrallah ne a garin Bazuriyah dake karkashin gundumar Sur a kudancin Lebanon, daga baya ya koma birnin Beirut da zama. Ya haifi ‘ya’ya 9, mata5 maza 4 daga cikinsu har da sayyid Hassan Nasrallah. A lokacin rayuwarsa ya kasance mahardacin littafin Allah mai tsarki, alkur’ani mai girma.