Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya yi barazanar kara kudaden fito kan kayakin duk wata kasa a duniya wacce ta sayarwa kasar Cuba man fetur.
Jaridar ‘The Nation ta kasar Amurka’ ta nakalto shugaban yana fadar haka a ranar laraba bayan ya sanya hannu a kan wasu takardu dangane da hakan.
Labarin ya kara da cewa kasar Mexico ce kasa ta farko wacce take sayarwa Cuba danyen manfetur, kuma itace ta samarda kashi 44% na man fetur da kasar Cuba ke bukata a shekara ta 2025 da ta gabata. Kafin haka kasar Venezuela ce take samar da wani bangare na makamashin da kasar Cuba take bukata. Amma bayan hare-haren da Amurka ta kaiwa kasar Venezuela a farkon wannan shekarar ta kuma sake shugaban kasa da matarsa zuwa Amurka kasar Cuba ta daina samun man fetur daga kasar.
A ranar Alhamis da ta gabata ce Trump ya zanta ta wayar tarho da shugaban kasar Mexico Claudia Sheinbaum, amma tace basu yimaganar kasar Cuba da shi ba, sannan basu yi maganai ma’adinai ba.
Kamfanin dillancin labaran Assosciated Press ya nakalto kamfanin man fetur na kasar Mexico ya na cewa, daga watan Jenerun shekara ta 2025 da ta gabata, zuwa 30 ga watan satumba na shekarar, kanfanin ya aika ganga 20,000 na man fetur zuwa kasar Cuba a ko wace rana.