Jami’ar Majalisar Dinkin Dunya ta yi kira da a dakatar da hulda da Isra’ila tare da neman a sauƙaƙe shigar da kayan agaji zuwa Gaza
Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya na Musamman kan yanayin kare hakkin dan adam a yankunan Falasdinawa da aka mamaye tun shekarar 1967, Francesca Albanese, ta bayyana cewa: Haratacciyar kasar Isra’ila ba ta da ikon doka na hana kungiyoyin agaji da ma’aikatan agaji shiga yankin Gaza da sauran yankunan Falasdinawa da aka mamaye.
A cikin wani rubutu da ta yi a dandalin X, Albanese ta yi kira ga kasashe da su dakatar da huldarsu da Haramtacciyar kasar Isra’ila har sai ta bi dokokin kasa da kasa, tare da la’akari da wannan matakin a matsayin wurin da za a samu zaman lafiya.
Ta kara da cewa, “Isra’ila ba ta da ikon doka na hana ma’aikatan agaji shiga Gaza da sauran yankunan Falasdinawa da aka mamaye. Mamaya ce ba bisa ka’ida ba, kuma dole ne ta kawo karshenta gaba daya ba tare da wani sharadi ba, kamar yadda Kotun Duniya ta tabbatar a shekarar 2024. Dole ne kasashe su dakatar da huldarsu da Isra’ila har sai Haramtacciyar kasar Isra’ila ta bi dokokin kasa da kasa.”
Jami’ar Majalisar Dinkin Duniya ta kuma yi magana kan kin Isra’ila na sabunta takardar izinin Olga Cherevko, mai magana da yawun Ofishin Majalisar Dinkin Duniya kan Harkokin Jin Kai (OCHA) a Gaza, wanda ya hana ta shiga yankin da aka killace.
Albanese ta ɗauki wannan matakin a matsayin wani ɓangare na tsarin takunkumi na zahiri da ake yawan yi wa ma’aikatan agaji na Majalisar Dinkin Duniya da na ƙasashen waje, “musamman waɗanda ake ganin suna da yawan bayyana ra’ayi game da abin da suke gani a ƙasa.”
Ta jaddada cewa ma’aikatan agaji “suna da alhakin bayar da shaida idan aka karya dokokin ƙasa da ƙasa.”