Nurul Mailki Na Iraki Ya Yi Watsi Da Tsoma Bakin Amurka A Harkokin Cikin Gidan Kasar

  Dan takarar sugabancin gwamnatin Iraki da Kawancen “Idharul-Tansiqi” na kasar ya tsayar,  Nurul-Maliki ya yi watsi da yadda Amurka take tsoma baki a harkokin kasar

  Dan takarar sugabancin gwamnatin Iraki da Kawancen “Idharul-Tansiqi” na kasar ya tsayar,  Nurul-Maliki ya yi watsi da yadda Amurka take tsoma baki a harkokin kasar dangane da wanda zai jagoranci gwamanti da wanda ba zai jagoranta ba.

Nurul-Maliki ya kara da cewa; Za su ci gaba da aiki tukuru har zuwa lokacin da za a tabbatar da cimma manufar maslahar koli ta al’ummar kasar Iraki.

Haka nan kuma Nurul-Maliki ya ce; Amfani da harshen tattaunawa a tsakanin kasashe shi ne kadai zabin siyasa.

Haka nan kuma ya nuna kin amincewa da yadda wata kasa za ta rika yin shifta akan abinda take son zai faru, yana mai yin watsi da tsoma bakin Amurka a harkokin cikin kasar Iraki, tare da bayyana shi a matsayin keta hurumin kasar Irakin.

Tun bayan da kawancen siyasa mafi gima na kasar Iraki ya gabatar da Nurul-Maliki a matsayin dan takarar mukamin Fira minista ne dai ,Amurka ta bakin ministanta na harkokin wajen Marco Rubio da shugaban kasar Donald Trump suke Magana akan cewa kasar za ta fuskanci takunkumai da takura.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted