Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta gayyaci Jakadan kasar Italia a nan Tehran zuwa ma’aikatar don jan kunnen jami’an gwamnatin kasarsa kan furucin da ministan harkokin wajen kasar yayi dangane da dakarun kare juyin juya halin musulunci a kasar wato IRGC.
Kamfanin dillancinlabaran IRNA na kasar Iran ya nakalto majiyar ma’aikatar na cewa a yau Talata ta kira jakadiyar kasar Italia a Tehran Paola Amadei zuwa ma’aikatar, inda mataimakin ministan harkokin wajen kasar kuma daraktan sashen yammacin Turai a ma’aikatar Iran Alireza Yousufi ya gabatar da korafin JMI dangane da furucin ministan harkokin wajen kasarsa kan rundunar IRGC.
Ma’aikatar ta kira jakadan ne rana guda bayan da ministan harkokin wajen kasar ta Italia Antonio Tajani ya yi kira ga tarayyar Turai ta zayyana dakarun IRGC a matsayin kungiyar yan ta’adda a duniya.
Yousefi ya yi amfani da kalamai masu zafi don nuna fushin JMI kan furucin ministan harkokin wajen kasar Itala kan dakarun IRGC wanda ya kasance bangare mai muhimmanci na jami’an tsaron JMI. Ya kuma bayyana shelanta dakarun IRGC a matsayin kungiyar yan ta’ada yana da maida martani mai tsanani. Daga karshe ya yi kira ga kasar Italiya su shiga taitayinsu dangane da kasar Iran.
Jakadiyar Italia a nan Tehran Paola Amedei, bayan zaman ta bayyana cewa za ta isar da sakon Iran ga gwamnatin kasar Italia.