Hizbullah: Sabon Yakin Amurka da Isra’ila Kan Iran Zai Kunna Wutar Yaki Ne A Yankin Yammacin Asiya

Babban sakatare janar din kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon shaikh Naimi Qasim yayi gargadin cewa harin Amurka da Isra’ila kan kasar iran zai fuskanci sakamako

Babban sakatare janar din kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon shaikh Naimi Qasim yayi gargadin cewa harin Amurka da Isra’ila kan kasar iran zai fuskanci sakamako mai tsanani ga dukkan yankin yammacin asiya, saboda Tehran za ta mayar da martani mai karfi kan duk wani wuce gona da irin akanta.

shaikh Na’im Qasim ya fadi hakan ne a wani jawabi da yayi da yammacin jiya litinin ga dubban alummar kasar labanon da suka taru a birnin berut babban birnin kasar labanon, inda mahalarta taron suka nuna goyon bayansu ga kasar iran, kuma suka nuna rashin amincewarsu ga barazanar da trump yayi wa jagoran juyin musulunci na iran Ayatullah sayed Ali Khamna’i.

haka zalika ya kara da cewa a kowanne lokaci kungiyar hizbullah tana goyon bayan Iran, da kuma jagoran juyi Ayatullah Khamna’I, kuma yace lokacin da trump yake barazana ga Ayatullah sayyid Khamna’I  to yana yi wa miliyoyin musulmi a fadin duniya ne da suke daukarsa a matsayin babban abin koyinsu a bangaren Addini.

daga karshe yayi tir da munafuncin kasashen yamma game da damuwa da hakkin alummar iran, kana yayi ishara game da goyon bayan da dinbin alummar kasar suke bawa jagoran juyin musulunci a kasar iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted