Fezeshkiyan Ya Shaidawa Takwaransa Na Rasha, Isra’ila Na Da Hannu Kai Tsaye A Rikicin A Iran

shugaban kasar iran Masoud Pezeshkiyan da na rasha Viladmir Putin sun tattauna ta wayar tarho a yau juma’a inda suka yi tsokaci game da tarzomar

shugaban kasar iran Masoud Pezeshkiyan da na rasha Viladmir Putin sun tattauna ta wayar tarho a yau juma’a inda suka yi tsokaci game da tarzomar da ta faru a kasar Iran a baya bayan nan, da kuma batun ci gaban yanki da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

wannan shi ne karon farko da aka tattaunawa ta wayar tarho tsakanin shuwagabannin kasashen biyu,bayan da Amurka da isra’ila suka goyi bayan tarzomar da ta faru a kasar iran, inda ko a taron gaggawa na kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya jakadan rasha ya zargi Amurka da tsoma baki cikin  harkokin cikin gidan iran wanda ya bayyana takunkumin da amurka ta kakabata mata a matsayin masomin zanga-zangar.

haka zalika Pezeshkiyan ta godewa Mosko game da goyon bayan da ta ke bawa iran a matakin kasa da kasa kuma ya fadi cewa kasashen Amurka da Isra’ila da wasu kasashen turai sun taka rawa wajen rikicin  da ya faru a baya bayan nan a iran, yace  gwamnati ta bullo da sabbin manufofi na cikin gida da nufin magance bukatun jama’a da kuma rage tasirin takunkumin da aka dade ana kakaba mata,

daga karshe Pezeshkiyan yayi ishara game da gangamin nuna goyon bayan gwamnati da aka gudanar bayan tarzomar, yana mai bayyanasu a matsayin shaida dake nuna cewa lamurra sun daidaita a kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted