rahotanni sun bayyana cewa kasar iran ta caccaki Amurka a lokacin zaman gaggawa na kwamatin tsaro na majalisar dinkin duniya, kuma ta zargi Amurka da hannu wajen tayar da tarzoma da karkatar da zanga-zangar lumana da aka yi, suma kasashen rasha da china sun yi watsi da tsoma bakin kasashen waje cikin harkokin cikin gidan Iran,
tattaunawar ta tabo kokarin da amurka ta yi na siyasantar da kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya da kuma tsoma baki cikin harkokin cikin gidan iran, hakan ya sa iran da wasu kasashe da dama suka sake Jaddada kaidojin ikon mallakar kasa, rashin tsoma baki da kuma girmama dokokin kasa da kasa.
mataimakin wakilin din din din na kasar iran a kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya Gholamhussain Darzi ya fadi cewa Washington ta tallafawa masu tada zarzoma a kasar Iran kuma ya bayyana bukatar da Amurka ta gabatar na tattaunawa a matsayin abin kunya.
wakilan kasashen baharain da liberiya sun jadda game muhimmancin mutunta gwamnatin kasar iranm kuma sun yi kira da a koma teburin tattaunawa, kuma suna adawa da duk wani mataki da zai kara tarwatsa yankin baki daya.