Ma’aikatar harkokin wajen rasha tayi soka mai tsanani game da tsoma baki da wasu kasashen waje suka yi a lokacin tarzomar da ta faru a baya bayan nan a kasar iran, kuma tayi gargadin cewa duk wani yunkurin fadada rikicikin to zai yi tasiri sosai a yammacin Asiya.
Wannan sakon ya zo ne A daidai lokacin da tarzoma ta barke a baya bayan nan a kasar iran wanda kai tsaye shugaban kasar Amurka da prime ministan isra’ila suke goyon baya.
Mariya zakharova kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar rasha ta fadi cewa mosko tayi tir da duk wata kasa dake tsoma baki cikin harkokin siyasar cikin gida ta kasar Iran, kuma ta zargi gwamnatocin kasashen yamma da yin amfani da dabarun juyin mulki wajen raunata karfin gwamnatin kasar iran.
Tace washington tayi barazanar daukar matakin soji kan kasar iran wanda lamari ne da bazaa taba amincewa da shi ba,ta kara da cewa wadanda suke son su yi amfani da hanyoyin tada tarzoma a cikin kasa a matsayin share fagen kai hari ya kamata su gane cewa akwai sakamako mara dadi da zai shafi tsaron yankin dama duniya baki daya.