Martani Mai Zafi Daga Ministan Tsaron Iran Zuwa Ga Shugaban Kasar Amurka Donald Trump

A jiya litinin ce shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi wa Jamhuriyar musulunci ta Iran barazanar kai mata harin soja, bayan ya ga

 A jiya litinin ce shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi wa Jamhuriyar musulunci ta Iran barazanar kai mata harin soja, bayan ya ga cewa miliyoyin mutane sun fito kan titunan biranen kasar suna nuna goyon baya ga gwamnatin kasar.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto ministan harkokin wajen kasar Iran wanda yake mayarwa trump martani kan barazanar kaiwa kasar wasu sabbin hare-hare. Ya ce duk wani harin da wani makiyi zai kawowa JMI ta iran zai gamu da maida martani mai zafi.

Donald Trump ya yi kira ga Iraniyawa yan ta’adda da su ci gaba abinda ya kira bore, domin yana nan zai kawo masu dauki nan ba da daewa ba.

Birgediya janar  Nasir Zadeh ya gargadi  shugaban kasar Amurka Donald Trump kan cewa; Idan har wauta da gigi su ka dauke ka, ka kawo wa Iran hare-hare- da ko wane irin dalili ne kuwa – to dukkanin maslahar  Amurka, a ko’ina suke a duniya, suna cikin hatsari.”

Ministan ya kuma kara da cewa; Duk wata kasa wacce ta taimakawa Amurka ko ta taimaka mata ta kawo wa Iran hari, ko ta bai wa Amurkan damar amfani da sansanoninta na soja, to ita ma wannan kasar ta halattawa Iran kaimata hare-hare.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted