Iran : Jagora ya yaba da gangamin kishin kasa da aka gudanar a duk fadin kasar

Jagoran juyin juya halin Musulunci, Ayatollah Seyyed Ali Khamenei, ya yaba da ganganmin kishin kasa da aka gudanar a duk fadin kasar don nuna goyon

Jagoran juyin juya halin Musulunci, Ayatollah Seyyed Ali Khamenei, ya yaba da ganganmin kishin kasa da aka gudanar a duk fadin kasar don nuna goyon baya ga tsarin Musulunci, yana mai cewa wannan gagarumin ya “kafa tarihi” kuma ya dakile shirin makiya na wargaza kasar.

Ayatollah Khamenei ya yi wadannan kalamai ne a ranar Litinin a cikin wani sako ga al’ummar Iran, bayan zanga-zangar da makiya suka shirya daga kasashen waje, inda mahalarta gangamin na kishin kasa suka yi Allah wadai da tarzomar da aka shirya daga kasashen waje, suka kuma sake jaddada goyon bayansu ga tsarin Musulunci.

Jagoran ya kara da cewa wannan gangamin ya nuna kishin kasa a gaban abokan gabansu, kuma hakan tamkar gargadi ne ga jami’an Amurka.

Ayatollah Khamenei ya bayyana al’ummar Iran a matsayin “masu karfi,” yana mai tabbatar da cewa suna nan a shirye kuma suna cikin shiri a duk wani lokacin rikici.

Zanga-zangar lumana kan matsalar tattalin arziki da aka soma a karshen watan Disamba a Iran ta rikide zuwa tarzoma, wadda ta samo asali daga kalamai ingizo daga hukumomin Amurka da Isra’ila, Inda bata gari da masu dauke da makamai suka lalata kadarorin jama’a tare da haddasa asarar rayuka tsakanin fararen hula da jami’an tsaro.

Kafin hakan dama a ranar Juma’a Ayatollah Khamenei ya bayyana cewa Jamhuriyar Musulunci “ba za ta ja da baya ba gaban masu masu zanga zangar da ake ingizawa daga kasashen waje ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted