Tarayyar Turai: Idan Amurka Ta Kwace Greenland Kungiyar Nato  Za Ta Rushe

Kungiyar tarayyar turai ta yi gargadin cewa, matukar Amurka ta kwace iko da yankin Greenland da karfin soja, to karshen kungiyar yarjejeniyar tsaro ta Nato

Kungiyar tarayyar turai ta yi gargadin cewa, matukar Amurka ta kwace iko da yankin Greenland da karfin soja, to karshen kungiyar yarjejeniyar tsaro ta Nato ya zo.

Jami’in kungiyar tarayyar turai mai kula da harkokin tsaro da kuma sararin samaniya Andrius Kubilius ya bayyana cewa; mamaye yankin na Greenland da Amurka za ta iya yi, yana nufin karshen Nato, kuma yana da mummunan tasiri akan rayuwar mutane.

Jami’in na tarayyar turai ya furta haka ne dai a yayin ganawarsa da manema labaru a kasar Sweeden, yana mai yin Ishara da matsayar da su ka cimmawa da Fira ministar kasar Denmark akan abinda zai iya faruwa ta fuskokin tsaro da kuma siyasa  idan Amurkan ta kwace Greenland.

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sha nanata cewa kasarsa za ta shimfida ikonta akan yankin na Greenland, cikin sauki da da karfi, domin idan ba su yi hakan ba, to  yankin zai shigar karkashin ikon Rasha da china, lamarin da ba za su taba lamunta da shi ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted