Ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi yace iran ta shiga wani sabon shafi mafi hatsari na hargitsi da aka fara tun daga ranar 8 ga watan janerun, bayan da yan ta’adda dauke da makamai suka kutsa tare da karbe zanga-zangar lumana da aka yi a fadin kasar suka zubar da jinanan mutane da kona wuraren gwamnati da na fararen hula.
Jamai’in yace kasancewar kungiyoyi dake dauke da makamai ya sanya zanga-zangar ta lumana ta canza zuwa ta taddanci, yana mai cewa kasar Amurka da isra’ila sune ke goyon bayansu a kokarin da suke yi na ganin bayan jamhuriyar musulunci ta iran, ta hanyar rikici bayan da suka gaza ta hanyar siyasa da kuma matsin lamba ta kafafen sadarwa.
Araqchi yayi wadannan bayanan ne a lokacin da yake ganawa da jakadu da jami’an diplomasiyar kasashen waje a nan birnin Tehran. Yace zanga-zanga tsakanin 8 zuwa 10 ga watan janeru an karkatar da ita ce daga manufarta ta asali ta hanyar kutsen masu dauke da makamai.
A yan kwanakin nan iran na fuskanta wani sabon lamari na rashen zaman lafiya da yan ta’adda dauke da makamai suka fara tarzoma a fadin kasar da suke samun dauki daga kasar Amurka da kuma HKI. Akwai hujjoji da suka hada da sautin da aka dauka da ake bada umarnin su harbe duk wanda suka samu a kusa da su ko farar hula ne , kuma da sannu zaa saki wadannan shedu a nan gaba.