Gwamnatin Sudan ta koma Khartoum bayan shekaru biyu na yaki

Gwamnatin Sudan ta koma Khartoum babban birnin kasar a hukumance bayan fiye da shekaru biyu na yakin basasa da ya daidaita kasar.   Firaministan Sudan

Gwamnatin Sudan ta koma Khartoum babban birnin kasar a hukumance bayan fiye da shekaru biyu na yakin basasa da ya daidaita kasar.  

Firaministan Sudan Kamel Idris ne ya sanar da hakan inda y ace gwamnatin kasar ta koma babban birnin inda zata maida hankali kan ayyukan inganta rayuwar jama’a.

Wannan shi ne karon farko tun bayan barkewar rikici tsakanin sojojin kasar da Rundunar Taimakon Gaggawa (RSF) a watan Afrilun 2023.

An tilasta wa gwamnatin Sudan barin Khartoum zuwa Port Sudan a farkon watannin yakin, a watan Afrilun 2023, kafin sojojin Janar al-Burhan su sami damar sake kwace iko, gundumomi bayan gundumomi, tsawon watanni na yaki, har sai da aka ayyana birnin a matsayin “an ‘yantar” da shi a watan Maris na 2025.

Gwamnatin ta Sudan ta yi alƙawarin dawo da ayyukan jama’a a babban birnin tare da sake gina asibitoci, makarantu, da hanyoyin ruwa, wutar lantarki, da tsafta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted