Shugaban Iran Ya Bukaci Masu Zanga Zangar Tsadar Rayuwa Kada Su Bawa Yan Ta’adda damar Shiga Tsakaninsu

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian yayi kira ga mutanen kasar wadanda suke zanga-zangar nemen kyautata rayuwarsu kada su bari yan ta’adda su shiga cikinsu, su

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian yayi kira ga mutanen kasar wadanda suke zanga-zangar nemen kyautata rayuwarsu kada su bari yan ta’adda su shiga cikinsu, su jawo tashe-tashen hankula su kuma haddasa matsalolin tsaro a kasar.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a yau Lahadi a hirar da ta hada shi da tasha ta labarai na IRIB a nan Tehran.

Shugaban ya kara da cewa mutanen kasar suna da hakkin bayyan damuwarsu wanda ya shafi tsadar rayuwa kuma gwamnatinsa a shirye take ta saurare su ta kyma yi aiki don don warware matsalolinsu. Amma su bambanta sahunsu da sahun wadanda suke son tada zaune tsaye a kasar ko kuma masu jawo matsalolin tsaro.

Shugaban ya yi kira ga iyaye Iraniyawa kada su bar yaransu su yaudaru da masu tada zaune tsaye da wadanda suke lalata dokokiyoyin gwamnati da kuma na mutane masu zaman kansu.

Ya ce makiyan JMI sun tarbiyantar da wasu mutane daga ciki da wajen kasar don lalata dukiyoyin al-umma su kuma kona kasar, har’ila yau su kashe mutanen kan mai uwa da wabi.

Daga karshe shugaban ya bayyana cewa dangane da tsadar rayuwa gwamnatinsa tana aiki dare da rana don tabbatar da cewa an warware wannan matsalar ta tsadar rayuwa da gaggawa. Yace makiya wadanda suka hada da HKI da Amurka sun shirya wargaza kasar, don haka kada mutane su basu damar yin hakan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted