Ministan tsaron kasar Somalia Ahmed Moalim Fiqi ya bayyana cewa HKI tana da shirin korar Falasdinawa daga yankin Gaza zuwa yankin Somaliland na kasar Somalia wanda yakeson ballewa daga kasar.
A wata hirar da ta hada shi da tashar talabijin ta Al-Jazeera na kasar Qatar Faqi yace yahudawan sun bukaci shugaban yankin Somaliland ya amince da wasu abubuwa uku na asali wadanda suka hada da amincewa da dawo da Falasdinawa daga Gaza zuwa Somaliland, kafa sansanin sojojin HKI a kasar da kuma shiga cikin shirin da suka kira ‘Yarcewyar Ibrahimiyya’.
Faqi ya ce Somaliland ta amince da wadannan abubuwan guda uku kafin HKI ta shelanta amincewar yankin a matsayin yentacciyar kasa.
Sai dai ministan harkokin wajen HKI Gidion Saar ya musanta shirin korar Falasdinawa daga Gaza da karfi zuwa kasar Somalia. A hirar da yayi da tasha ta 4 da haramtacciyar kasar.
Kafin haka shugaban kasar Somalia Hassan Sheikh Mohamud ya bayyana cewa baya son HKI ta dawo da rigimarta da Falasdinawa zuwa kasar. Sannan ya bukaci HKI ta janye amincewa da Somaliland a matsayin yentacciyar kasa daga Somalia.