IRGC: Muna Tare Da Al’ummar Iran Har Zuwa Lokacin Murkushe Manufofin Makiya

Hukumar leken asirin dakarun kare juyin juya halin musulunci ta Iran ta bayyana cewa; Bayanan sirri da ake da su, sun tabbatar da cewa, abokan

Hukumar leken asirin dakarun kare juyin juya halin musulunci ta Iran ta bayyana cewa; Bayanan sirri da ake da su, sun tabbatar da cewa, abokan gaba sun sauya salon yaki da Iran daga kawo hari kai tsaye, zuwa tayar da hargitsi a cikin gida.”

 Bayanin ya ci gaba da cewa; Bayan da makiya su ka ci kasa wajen tilasatawa jamhuriyar musulunci ta mika wuya, Amurka ta mayar da hankali wajen jefa Iran cikin yanayin yaki da kuma sake dawo da takunkumai akan Iran masu tsanani, sannan kuma da yin kira ga mabarnata da su fito domin haddasa hargitsi.

Haka nan kuma ya kara da cewa; makiyan sun Shata manufofi mabanbanta da su ka hada kungiyoyin leken asiri na waje da suke aiki da wasu gurbatattun mutane, haka nan kuma wasu kungiyoyi masu dauke da makamai ‘yan ta’adda.

Wani sashe na bayanin dakarun kare juyin musulunci ya kunshi yin tsokaci akan yadda shugaban kasar Amurka yake Magana a cikin wauta ta nuna goyon bayan masu tarzoma da ‘yan ta’adda.

Haka nan kuma bayanin ya yi Magana akan yadda masu tarzomar suke kai hare-hare akan sansanonin soja, ofisoshin ‘yan sanda da hakan ya yi sanadiyyar shahadar mutane da dama, da jami’an tsaro.

Dakarun kare juyin musuluncin na Iran sun kuma tabbatar da cewa suna tare da al’ummar kasa har zuwa lokacin murkushe makiya abokan gaba.

 Ita ma rundunar sojan Iran ta fitar da nata bayanin da ya kunshi cewa za su kare cibiyoyin kasa daga mabarnata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted