Sojojin Kasar Lebanon Sun Kammala Aikin Takaita Makamai A Hannun Gwamnati A Kudancin Kasar

Majiyar sojojin kasar Lebanon ta bada sanarwan cewa sun kammala aikin tattara makamai, ko kuma takaitasu a hannun gwamnati a kudancin kasar kamar yadda ya

Majiyar sojojin kasar Lebanon ta bada sanarwan cewa sun kammala aikin tattara makamai, ko kuma takaitasu a hannun gwamnati a kudancin kasar kamar yadda ya dace.

Shafin yanar gizo na labarai ArabsNews na kasar Saudia ya nakalto majiyar sojojin na fadar cewa banda karban makamai da kuma kwance boma boman da basu face ba sun karbi dukkan makaman da suke hannun mutane a yankin. Abinda ya rage kadai inji rahoton a kwai wasu ramukka wadanda na karkashin kasa a yankin wadanda yakamata su yi aiki a kansu.

Tun bayan yakin da kungiyar Hizbullah ta shiga da HKI don tallafawa Gaza da kuma shahadar Sayyid Hassan Nasarallah ne, aka zabi shugaban kasa a kasar ta Lebanon wacce daga baya ta kudurin anniyar kwance damarar kungiyar Hizbullah tare da bukatar Amurka da HKI.

A cikin yakin shekara guda da watanni da suka fafata, sojojin HKI sun kasa mamayar kasar Lebanon duk tare da makaman zamanin da suka mallaka. A wannan sanarwan ta sojojin kasar dai basu ambaci kungiyar Hizbulla da kuma makamansu ba.   

A cikin watan Nuwamban shekara ta 2024 ne dai HKI a dole da kulla yarjeniyar tsagaita budewa Juna wuta da kungiyar Hizbullah, ammam tun lokacin har yanzun basa mutunta yarjeniyar. Suna kuma ci gaba da kai hare-hare kan kasar ta Lebanon musamman kudancin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted