Ana sa ran kamfanoni da matatun mai na China za su kara yawan man da suke shigowa da shi daga Iran a daidai lokacin da rikicin Venezuela ya jefa jigilar danyen mai daga kasar cikin hadari.
Rahoton da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya fitar a ranar Laraba ya ce ana sa ran kamfanonin matatun mai na China, wadanda galibi ke sayen mai daga kasashen da Amurka ta sanya wa takunkumi, ciki har da Rasha, Iran, da Venezuela, za su kara yawan man da suke shigowa da shi daga Iran a cikin watanni masu zuwa.
Rahoton ya ce kayayyakin Iran za su maye gurbin kayayyakin Venezuela da aka dakatar bayan da Amurka ta kai hari kan Venezuela a karshen mako tare da sace Shugaban kasar, Nicolas Maduro.
Rahotanni sun nuna cewa babbar tashar jiragen ruwa ta Venezuela ta dakatar da jigilar danyen mai zuwa Asiya tun farkon watan Janairu.
Reuters ta ambato manazarta kasuwa suna cewa masu matatun mai na China za su iya komawa ga kayayyakin Iran daga nan zuwa watanin Maris da Afrilu, ciki har da siyan man da aka sanya wa takunkumi daga kasar.
Iran ta kasance babbar mai samar da mai ga matatu masu zaman kansu a China a cikin ‘yan shekarun nan, inda rahotanni ke nuna cewa jigilar mai ta wuce ganga miliyan 2 a kowace rana daga Iran zuwa China a cikin watannin da suka gabata.
Venezuela, wacce ita ce kasar da tafi kowace kasa yawan danyen man fetur da ke kwance a karkashin kasa a duniya, ta kasance karkashin manyan takunkumai na Amurka tsawon lokaci, wanda hakan ya kawo cikas matuka ga ayyukanta na fitar da danyen mai zuwa kasashen duniya.