Burkina Faso: An Zargi Kanar Damiba Da Yunkurin Yi Wa Shugaba Traore Juyin Mulki

Gwamnatin Burkina Faso ta sanar da dakile yunkurin juyin mulki da aka shirya  wa Shugaba Ibrahim Traoré, tana zargin tsohon shugaban riƙon ƙwarya, Kanar Paul

Gwamnatin Burkina Faso ta sanar da dakile yunkurin juyin mulki da aka shirya  wa Shugaba Ibrahim Traoré, tana zargin tsohon shugaban riƙon ƙwarya, Kanar Paul Henri Sandogo Damiba, da hannu a cikin Shirin.

Ministan Tsaron Burkina Faso Mahamadou Sanna ya bayyana a wani taron manema labarai cewa, makircin wanda aka shirya a daren Asabar, an wargaza shi “saboda ƙwarewar hukumomin leƙen asiri.” Ya ƙara da cewa “shirin ya haɗa da jerin kisan gilla a kan sojoji da farar hula, wanda ya fara da yunƙurin kashe Traoré, ko dai a kusa ko kuma ta hanyar dasa abubuwa masu fashewa a gidansa.”

Ya ƙara da cewa, “Bayan haka, an shirya wani aiki don rusa e sansanin jiragen sama marasa matuƙa, sannan kuma sojojin ƙasashen waje su shiga cikin kasar da sunan shiga Tsakani ko wanzar da zaman lafiya.”

Ya bayyana cewa “an ba wa sojojin da ke cikin wannan shiri  aikin ɗaukar wasu rundunonin sojoji da kuma kafa wasu ƙungiyoyi, yayin da fararen hula za su tattara magoya baya don tallafawa wajen karɓe iko bayan matakin soja.”

Ya jaddada cewa “ana ci gaba da gudanar da bincike da kama wadanda ake zargin suna da hannu kai tsaye a cikin lamarin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted