Rahotanni sun bayyana cewa ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa harkokin cikin gidan kasar iran na alumarta ne don haka yana tir da tsoma baki da wasu ke yi cikin abubuwan da bai shafe su ba, kuma iran bata bukatar wani ya tsoma mata baki cikin harkokinta,
Har ila yau ya kara da cewa harkokin cikin gida na kasar iran ya shafi iraniyawa ne kawai, duk wani yunkurin kasashen wajen na shiga shugala ba za’a amince da shi ba, don haka gwamnatin tana aiki da mutane wajen ganin an shawo kan duk wani lamari, kuma babu wani daga waje dake da hakkin ya fada mana abin da za mu yi.
Haka zalika yayi tir da mataken rashin dattako da Amurka take dauka wanda su ne suka sanya aka kasa samun ci gaba mai ma’ana a tattaunawar, yace yanzu ba lokacin tattaunawa ba ne kuma ya faru ne saboda irin tsarin Kasar Amurka , amma bamu taba barin teburin tattaunawa ba, ko wane lokaci a shirye muke mu tattauna amma bisa mutunta juna, sabanin abin da Amurka take yi.