Rahotanni sun bayyana cewa kasar rasha ta aike da jiragen ruwa na yaki da sauran makamakan sojojin Ruwa domin raka tankokin manta adaidai lokacin da sojin ruwan Amurka suke kokari kwace tankokin mai a arewacin tekun Atilantika, kuma tankokin na rasha suna kan hanyarsu ta zuwa gabar tekun Murmansk ne.
Jiragen sama na yaki na Amurka suna ta shawagi a rewacin Atilantika tun da sanyi safiyar yau, suna tunkarar tankokin mai da suke zatun suna zuwa ne daga Marinera, jiragen ruwan suna tafiya yanzu haka tsakanin Icelanda da birtaniya, washington tana zargin jiragin ruwa ya keta takunkumin Amurka inda yake dakon manfetur din kasar Iran,
Ministan harkokin wajen kasar Rasha ya bayyana cewa suna ci gaba da bibiyar halin da tankokin mai suke ciki a yankin, yace ba tare da wani dalili ba an sa ido kan tankokin mai kasar rasha duk da yake cewa ana zaune lafiya, lamarin da ya dauki hankalin sojojin Amurka da nato, mosko tana sa ido ko kasashen yamma za su mutunta yancin zirga ziegar jiragen ruwa.