Fadar mulkin kasar Amurka ta sanar da cewa, shugaban kasar Donald Trump yana tattauna yadda za a yi kasarsa ta shimfida ikonta akan yankin Greenland, ko da kuwa za a yi amfani da karfin soja ne.
Bayanin fadar mulkin na kasar Amurka ” White House” ya kuma ci gaba da cewa; shugaban kasar ya riga ya bayyana cewa shimfida iko akan yankin na Greenland yana da alaka ne da tsaron kasar Amurka, kuma wajibi ne domin takawa abokan jayayyar Amurka birki a yankin dungun duniya na arewa.
Bayanin ya kuma ce; shugaban kasar da tawagarsa suna tattauna yadda za a cimma wannan manufa wanda shi ne abu mai muhimmanci a siyasar waje, kuma a kowane lokaci amfani da karfin sojan Amurka, wani abu ne da yake a karkashin ikon babban kwamandan dakarun sojan kasar.
A jiya Talata wani jami’in gwamnatin Amurka ya sanar da cewa, hakkin kasarsa ne ta mallaki tsibirin “Greenland’ yana mai kore cewa da akwai wanda zai iya yakar Amurka saboda wannan yanki.
Mai bai wa shugaba kasar Amurka shawara akan harkokin tsaron kasa Stephen Miller ya yi tambayar cewa; me zai sa ace kasar Holland ce ta mallaki wannan yankin?
Da aka tambaye shi, ko Amurka za ta yi amfani da karfin soja domin cimma wannan manufa? Miller ya ce; ko kadan ma bai kamata a yi wannan tunanin ba, domin babu wata kasa wacce za ta yaki Amurka saboda wannan yankin.
A ranar Litinin din da ta gabata mai dai shugaban kasar Amurka ya ce; Amurka tana da bukatar wannan yankin, wanda yake zagage da jiragen Rasha da China.