Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Baqir Qalibof, ya bayyana cewa, tare da abinda Amurka ta aikata a kasar Venezuela ankawo karshen dokokin kasa da kasa kuma.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Qalibof yana fadar haka a taron babban zauren majalisar dokokin kasar Iran a yau litinin. Ya kuma kara da cewa karfin kasar Iran ya dogara da Allah da farko sannan hadin kan mutanen kasar, da kuma kyautata tattalin arzikin mutane, da tsaro da kuma takaita rashin daidaito tsakanin mutanen kasar.
Ya kara da cewa makiya zasu sha kaye a duk wani harin da zasu kawowa kasar, saboda mafarki ne suke idan suna ganin zasu kawo karshen JMI.