Iran Ta Gargadi Hukumar IAEA Kan Barazanar Trump Kan Cibiyoyin Nukliyarta

Jakadan kasar Iran a cibiyoyin MDD da kuma kuma sauran cibiyoyin kasa da kasa a Geneva ya gargadi hukuma mai kula da makamashin nukliya ta

Jakadan kasar Iran a cibiyoyin MDD da kuma kuma sauran cibiyoyin kasa da kasa a Geneva ya gargadi hukuma mai kula da makamashin nukliya ta duniya wato IAEA kan cewa barazanar da shugaban kasar Amurka yakewa cibiyoyin makamashin nukliya na kasar Iran, barazana ce ga hukumar kanta.

Saboda idan Amurka zata yi gabanta ta yi abinda ta ga dama, sannan hukumar IAEA ta yi gum da bakinta ta kasa yin ko allawadai da ita to kuwa yarjeniyar NPT ta tashi daga aiki, kuma hukumar IAEA ta rasa madafa ta samuwarta. 

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto jakadan a wasikar da yarubutawa Rafael Grossi babban daraktan hukumar ta IAEA, yana cewa idan baya zai iya yin ko allawadai da furin shugaban Amurka na barazana ga cibiyoyin nukliyar wata kasa a duniya ba, wace kasa kuma a duniya zata sake amincewa da samuwar hukumar IAEA da manufofin aiwatar da yarjeniyar NPT? Babu.  

 Labarin ya kara da cewa shugaban kasar Amurka Donal Trump a wani jawabin hadin giwa da firai ministan HKI a jiyar Florida ta kasar Amurka a ranar Litinin da ta gabata, yayi barazanar shafe dukkan cibiyoyin nukliyar kasar Iran idan ta yi kokarin sake farfado da cibiyoyinta na tashe makamashin Uranium ko kuma makamanta masu linzami. 

Amma a ranar Talata shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiya ya mayarwa shugaban martani inda yake cewa duk wani harin da Amurka ko Isra’ila suka sake kawowa kan Iran zai gamu da maida martani mai tsanani, mai kuma sanya nadama ga duk wanda ya kawo harin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted