A dai dai tsakiyar daren jiya ne aka fara bukukuwan shigar sabuwar shekara ta 2026 a nan Tehran da kuma garuruwan da kiristoci suke zama a duk fadin Iran.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shirin da aka gudanar a cocin Targ-manchat da kan titin Wahidi a dai dai shigowar sabon shekara wato 1 ga watan Janerun shekara ta 2026. Inda wannan cocin, banda kasancewar sa coci, har’ila yau ya zama wurin tunawa da samuwar kiristoci a kasar Iran na lokacin mai tsawo saboda tsufar ginin cocin.
Labarin ya kara da cewa an gina cocin tun shekara 1968 tare da taimakon majalisar cocuna ta duniya da kuma Armaniyawa mazauna birnin Tehran.
Cocin ya zama mafaka ga kiristoci wadanda girgizan kasa ta tilasta masu kaura daga garin Buin Zahra da ke arewacin kasar Iran a shekara 1962.
Yawan kiristoci a kasar Iran dai ya kusan dubu 200, kuma suna da wakilci a majaliasar dokokin kasar, a matsayin kananan addinai da kabilun da kundin tsarin mulkin kasar Iran ta amince da samuwarsu.