Iran ta ayyana rundunar sojojin ruwa ta Royal Canada a matsayin kungiyar ta’addanci a hukumance a matsayin maida martani ga gwamnatin Canada data ayyana dakarun kare juyin juya halin Musulinci na Iran IRGC a matsayin kungiyar dake goyan bayan ta’addaci.
A cikin wata sanarwa, Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana cewa an ɗauki wannan matakin ne a matsayin ramuwar gayya” da kuma martani ga ayyana (IRGC) da Amurka ta yi a matsayin kungiyar ta’addanci, wannan kuma Canada ta bi sahun Washinbgton.
Ma’aikatar ta bayyana cewa shawarar Ottawa kan Rundunar dakarun kare Juyin Juya Halin Musulunci, “wanda ke matsayin ginshikan rundunar sojojin kasar,” ya saba wa ka’idodin dokokin kasa da kasa.
A cewar sanarwar, Iran ta yi hakan ne a matsayin mayar da martani bias tanadin mataki na 7 na dokar 2019, wanda ya tanadi cewa “dukkan kasashen da suka bi ko suka goyi bayan shawarar Amurka ta ayyana IRGC a matsayin kungiyar ta’addanci za a dauki matakin mayar da martani.”
Ma’aikatar Harkokin Waje ta bayyana cewa wannan shawarar ta Otawa na a matsayin alama ta ci gaba da nuna kiyayya da ga Tehran.
A shekarar 2012, Canada ta yanke dangantakar diflomasiyya da Iran kuma ta rufe ofishin jakadancinta a Tehran, tana fakewa da dalilai daban-daban, da suka hada da goyon bayan Iran ga Siriya, shirin nukiliyarta, da kuma barazanar da ake yi wa gwamnatin Isra’ila.