Rahotanni sun bayyana cewa shugaban majalisar shawarar musulunci na iran mohammad baqer qalibaf yayi gargadin cewa alummar iran a shirye suke su mayar da martani kan duk wani wuce gona da iri, kuma zai kasance mai fadi ba tare da yin sulhu ba, kuma ba zato ba tsammani, domin Tehran bata neman izinin kowa don kare kanta
Shugaban ya fadi hakan ne a majalisa a jiya talata, kuma ya zayyana matsayar iran wajen kare kanta,kuma ya bayyana irin nasarorin da kasar ta samu a baya-bayan nan na harba tauraron dan adam a sararin samaniya wanda dukkansu an yi su ne a cikin gida,
Haka zalika ya jinjinawa matasa masana ilimin kimiyya game da nasarar da suka samu na harba taurarun dan Adam, kuma yace wadannan matasan za su iya warware matsaloli masu yawa da kasar ke fuskanta inda aka basu dama.
Daga karshe yace matakin da iran za ta dauka wajen kare maslaharta ta hanyar amfani da hakkinta halastace wajen kare kanta, ba lamari ne da za’a iya tsinkayarsa ba ko kuma ya zama daidai da wanda ya gabace shi.