Iran Ta Shelanta Sojojin Ruwa Na Kasar Canada A Matsayin Sojojin Yan Ta’adda

Gwamnatin kasar Iran a hukumance ta shelanta sojojin ruwa na kasar Canada wato (Royal Canadian Anavy) a matsayin sojojin yan ta’adda kamar yadda gwamnatin kasar

Gwamnatin kasar Iran a hukumance ta shelanta sojojin ruwa na kasar Canada wato (Royal Canadian Anavy) a matsayin sojojin yan ta’adda kamar yadda gwamnatin kasar Canada ta zayyana wani bangare na sojojin kasar Iran.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ma’aikatan harkokin wajen kasar Iran na fadar haka a yau Talata a nan Tehran. Ta kuma kara da cewa ta gana wannan hukuncin ne bisa doka wacce ta maida martani ga Amurka wacce ta zayyana dakarun IRGC a matsayin kungiyar yan ta’adda, wannan dokar an fadadata ta kuma hana har da sojojin ruwa na kasar Canada.

Ma’aikatar ta kara da cewa Ottawa ta zayyana IRGC a matsayin kungiyar yan ta’adda al-hali sune gintsikin sojojin kasar Iran, wanda hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa. Wato wata kasa ta shi sojojin wannan kasa yan ta’adda ne wannan kwace diyauci ne daga hannun kasar. Don haka hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa. Kuma shi ya sa mukadauki wannan matakin na maida martani.

Bayanin ya kara da cewa gwamnatin Iran ta yi amfani da doka da 7 ta shekara 2019 wacce ta bayyana cewa ‘Duk wata kasa a duniya wacce ta ke goyon bayan Amurka wajen zayyana dakarun IRGC a matsayin kungiyar yan ta’adda itama za’a maida mata martani irinsa’.

Bisa wannan dokar daga yau JMI tana daukar sojojin ruwa na kasar Canada mai suna ‘Rayal Canadian Navy’ a matayin kungiyar yan ta’adda.

A shekara ta 2012 ne kasar Canada ta rufe ofishin jakadancinta a Tehran tare da zargin Iran da goyon bayan gwamnatin kasar Siriya, rashin amincewa da shirinta na makamashin Nukliya da kuma barazana ga HKI. Sannan a shekarar ne ta fidda kungiyar yanta’adda Iraniyawa MKO daga jerin kungiyoyin yan ta’adda a wajenta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted