Kungiyarta Kurdawa ta “Syrian Democratic Forces” ta sanar da cewa shugabanta Mazlum Abdi ba zai je birnin Damascuss ba, saboda wasu dalilai na tsarin aiki.
A yau Litinin ne dai kungiyar ta ce; A yau Litinin 29/Disamba 2025 aka shirya cewa Mazlum tare da masu yi masa rakiya za su tafi birnin Damascuss, sai dai kuma an dage ziyarar saboda wasu dalilai na aiki, amma nan gaba za a sake ayyana lokaci idan an cimma matsaya tsakanin bangarorin biyu.”
Haka nan kuma bayanin ya ce, manufar ziyarar ita ce tattauna hanyoyin da za a shigar da mayakan nasu a cikin cibiyoyin hukumar Syria daga ciki har da ma’aikatun tsaro da kuma ta cikin gida.
A ranar 10/Maris ne dai aka kulla yarjejeniya aiwatar da shigar da mayakan na Kurdawa a cikin cibiyoyyin gwamnati, wanda wa’adinsa yake karewa.
A cikin kwanakin nan ma dai an yi taho mu gama a tsakanin mayakan na kungiyar “Syrian Democratic Forces” da kuma jami’an tsaron Syria a cikin birnin Halab.
An yi musayar wuta, wacce ta tilastawa mutanen cikin unguwannin da lamarin ya faru, yin hijira.
A wasu labaran da suke fitowa daga kasar ta Syria, an ji karar fashewar wasu abubuwa a unguwar Mizzi dake cikin birnin Damascuss.