Al’ummar Gaza Na Fuskantar Mastalar Haihuwa da Kisan Kiyashin Isra’ila

Hukumomin lafiya a yankin Gaza sun bada rahoton raguwar yawan haihuwa da kuma karuwar yin barin ciki , wanda rashin abinci mai gina jiki ,

Hukumomin lafiya a yankin Gaza sun bada rahoton raguwar yawan haihuwa da kuma karuwar yin barin ciki , wanda rashin abinci mai gina jiki , damuwa da kuma takaita yadda za’a samu kula da lafiya , adaidai lokacin da isra’Ila ke kisan Karen dangi a yankin.

Kamar yadda bayanan da ma’aikatar lafiya ta yankin falasdinu ta bayyana ya nuna cewa yara 17000 ne kawai aka Haifa a farkon shekara ta 2025 da yake nuna samu raguwa da kasha 41% idan aka kwatanta da irin wannan lokaci a shekara ta 2022 inda akalla a aka haifi jarirai 29000.

Kungiyoyin majalisar dinkin duniya da suka hada da UNFPA da kuma UNICEF sun hada wadannan kididdigar kuma sun bayyana yanayin a a matsayin babban bala’I ga mata masu ciki da ma jarirai sabbin haihuwa.

Hukumomin jin kai na duniya sun yi kira da a dauki tsauraran mataken gagawa wajen bada agajin da ya dace ,yace za’a fuskanci mummunan sakamako ga dukkan alummar yankin idan ba’a canza yanayin ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted