Somaliya da wasu manyan kasashen yankin sun yi Allah wadai da Isra’ila kan amincewa da Somaliland a matsayin kasa mai cin gashin kanta.
A jiya ne gwamnatin Isra’ila ta sanar da amincewa da Jamhuriyar Somaliland da ta ayyana kanta a matsayin kasa mai cin gashin kanta.
Somaliya da wasu manyan kasashen yankin sun yi Allah wadai da wannan shawarar, wadanda suka yi gargadin cewa ta karya dokokin kasa da kasa kuma tana barazana ga zaman lafiyar yankin.
Ofishin Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa Tel Aviv ta amince da Somaliland a matsayin “kasa mai cin gashin kanta ” kuma ta sanya hannu kan wata yarjejeniya da nufin karfafa dangantaka tsakanin bangarorin biyu.
Isra’ila dai ta zama kasa ta farko da ta amince da Somaliland a hukumance a matsayin kasa.
Ofishin Netanyahu ya kira “Yarjejeniyar Abraham,” wadda Donald Trump ya shiga tsakani a lokacin wa’adinsa na farko, a matsayin tushen amincewar Tel Aviv da Somaliland a matsayin kasa.
Tuni Abdirahman Mohamed Abdullahi, wanda ya ayyana kansa a matsayin shugaban Somaliland, ya yi maraba da shawarar Isra’ila, yana mai bayyana hakan da abu mai tarihi.
Kasashen Somaliya, Masar, Turkiyya, da Djibouti sun yi Allah wadai da wannan mataki na Isra’ila.
Kafin hakan, gwamnatin Sahayoniya ta dauki Somaliland a matsayin wurin da za ta jibge Falasdinawa bayan korarsu.
Haka zalika gwamnatin Isra’ila na da niyyar gina sansanin soja a Somaliland, wanda zai bai wa sojojina a yankin damar kwace iko da Tekun Aden tare da kai hari kan gwamnatin Yemen da Ansarullah ke jagoranta.