Aljeriya Ta ayyana mulkin mallakar Faransa a matsayin babban Laifi

Majalisar Dokokin Aljeriya ta amince da wata doka da ta ayyana mulkin mallaka na kasar Faransa a matsayin babban laifi tare kuma da bukatar Faransar

Majalisar Dokokin Aljeriya ta amince da wata doka da ta ayyana mulkin mallaka na kasar Faransa a matsayin babban laifi tare kuma da bukatar Faransar ta nemi afuwar kasar a hukumance.

Matakin dai na zuwa ne a daidai lokacin da dangantakar difflomatsiyya tsakanin Algers da Paris ke kara tsami.

Daftarin dokar dai na daga cikin bukatar kasra ta Aljeriya na ganin tashin hankali da ababen da suka tattare da shi a lokacin mulkin mallaka na Faransa a Aljeriya daga 1830 zuwa 1962, ya kasance cin mutunci da zarafi da kuma hurumin kasar ta Aljeriya wanda kuma ya kamata faransa ta nemi afuwa akansa.

Akan hakan majalisar dokokin Aljeriya, ta bukaci faransa da ta “biya” diyya ga mulkin mallakar, gami da sabtace wuraren da faransa ta yi gwajin nukiliya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted