Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa diblomasiyya ba shi ne aika boma bomai ba, kamar yadda gwamnatin Amurka take son mu fahinta.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalyo Jakadan kasar Amurka a MDD Morgan Ortagus yana fada a wani taron kwamitin Tsoro na majalisar a farkon wannan makon, kan cewa yana kiran kasar Iran zuwa tattaunawa kai tsaye da Amurka don kaucewa wuta.
Abbas Aragchi yana mayarwa Morgan Ortagus martani ne a shafinsa na X, ya kuma kara da cewa, wannan shi ne diblomasiyyar kasar Amurka tana kira ga Iran ta amince da tattaunawa kai tsaye da ita don kaucewa wutan Amurka. Aragchi wannan a fahintarmu ba shi ne ake kira diblomasiyya ba. Wannan aka kiransa tursasawa.
Ya ce Amurka tana son ta hana mutanen kasar Iran hakkinsu wanda dokokin kasa da kasa suka amince mata, kuma idan ta ki amincea da hakan tana mata barazanar data yi amfani da karki don tilastawa Iran amincewa da abinda take so.
Ortagus ya bayyana haka ne a ranar 23 gawatan Decemban da muke ciki a kwamitin tsaro na MDD inda Amurka da wasu kasashen turai suka bukaci a farfado da kuduri mai lamaba 2231 ta shirin Nukliyar kasar Iran amma saboda rabuwar kai a kwamitin wannan bukatar ta kasa wucewa.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa ” Tursasawa ba tattaunawa ba’ Iran a matsayinta na kasa mai yencin kanta ba zata tana amincewa da tursasawa a kan hankinta ba. Kuma barazana ba zai taba amfani a kanta ba. Ba zata taba barin hakkin mutanenta da mallakar fasahar Nukliya wacce yarjeniyar NPT ta amince mata don biyan bukatar Amurka ba.