Makami Mai Linzami Na Kasar Iran Ya Shiga Ta Windon Ofishin Shugaban Leken Asiri Na Sojojin HKI

Kakakin sojojin kasar Iran Burgedia Janar Abolfadle Shekarchi ya bayyana cewa a cikin yakin kwanaki 12 na yakin da Amurka da HKI suka dorawa JMI

Kakakin sojojin kasar Iran Burgedia Janar Abolfadle Shekarchi ya bayyana cewa a cikin yakin kwanaki 12 na yakin da Amurka da HKI suka dorawa JMI a cikin watan Yulin da ya gabata, daya daga cikin makamai masu linzamin sojojin Iran ya shiga ta windon ofishin shugaban bangaren leken asiri na sojojin HK, ya kuma rusa ginin gaba daya.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya nakalto Janar Shekarchi yana fadar haka a jiya Talata, a lokacinda yake bayyana gazawar garkuwan makaman kasar Amurka da ake kita THAAD ‘ wanda suke tutia da shi wajen kakkabo makamai a sama, ya ce makamai masu linzami na kasar Iran suna da kayakin aiki wadanda na farko suke basu damar fadawa a inda ake son su fada ba tare da kuskuren a zo a gaini ba. Banda haka makaman suna da kayan aikin da garkuwan makaman Amurka mafi inganci, wato THAAD sun kasa kakkabu shi.

Ya ce ana saida garkuwan makamai ta THAAD (Terminal High Altitude Area Defense) system kan dalar Amurka miliyon $10 zuwa miliyon $12 ko wani daya.

Shekarchio ya bayyana cewa daga farkon yakin kwanaki 12 zuwa yanzun,  jami’an tsaron JMI sun kama Iraniyawa kimani 2000 wadanda suke aikin leken asiri wa HKI a kasar.  

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted