Hukumomin Gaza sun ce fiye da Falasdinawa 410 ne aka kashe, wasu 1,112 kuma suka jikkata a hare-haren Isra’ila a Gaza tun bayan da yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki a ranar 10 ga Oktoba.
Ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza ya ba da rahoton cewa, laifuka 875 Isra’ila ta aikata a yarjejeniyar, ciki har da hare-hare kai tsaye 265 kan fararen hula, hare-haren soji 49 a yankunan zama, hare-haren bama-bamai 421, da rushe gidaje 150.
A sabon harin da suka kai, sojojin gwamnatin mamaya sun harbe Falasdinawa biyu har lahira a unguwar Shuja’iyya, dake gabashin birnin Gaza.
Waɗannan mace-macen sun kawo jimillar adadin Falasdinawa da aka tabbatar sun mutu a Gaza a cikin awanni 24 da suka gabata zuwa akalla 12, ciki har da gawawwaki takwas da aka gano daga tarkace a fadin yankin.
Tun daga watan Oktoban 2023, sojojin Isra’ila sun kashe Falasdinawa kusan 71,000, galibi mata da yara, tare da raunata sama da 171,000 a hare-haren da suka kai a Gaza.
Ofishin ya zargi Isra’ila da gaza cika abunda ya wajaba a gare ta a karkashin yarjejeniyar tsagaita wutar, inda ya yi kira da a tabbatar da “samar da agajin jin kai da mai, da kuma shigar da tantuna, gidajen zama, karafa, da kayan mafaka, kamar yadda aka tsara a cikin yarjejeniyar, domin magance matsalar jin kai da ke kara ta’azzara a Zirin Gaza.”