Shugaban kasar Ukraine Volodimir Zelesky ya bada sanarwan cewa, ya sami nutsuwa kan cewa kasarsa zata kasance cikin amince daga kasar Rasha idan an dakatar da yaki, daga Amurka da kuma kasashen Turai.
Tashar talabijin ta Al-Mayadin ta kasar Lebanon ta kara da cewa, shugaban ya ce gwamnatin Amurka ta bada lamunin tabbatar da tsaron kasar Ukraine a duk lokacinda aka tsagaita wuta ko aka kawo karshen yaki a Ukraine, sai dai ba zai iya bayyana wasu daga cikin matkan tsaron da Amurkan zata dauka don tabbatar da zaman lafiya a kasar ba.
Labarin ya nakalto mai bawa gwamnatin kasar Jamus shawara kan al-amuran tsaro yana cewa Amurka da kasashen Turai sun cimma yarjeniyar samar da tsaro wa kasar Ukraine bisa tsarin tsaron da ke karkashin kungiyar tsaro ta NATO idan har bukatar hakan ta taso.
A dayan bangaren kuma ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta bada sanarwan cewa Rasha ta Amurka cimma matsaya kan yadda kasar Ukraine zata kuma kamar yadda take. Ba tare da mallakar makaman nukliya ba.