Amurka Tana Kokarin Kwace Wata Tankan Mai Ta Venezuela Na Uku

Gwamnatin shugaban kasar Amurka Donal Trump ta kara karfi wajen tabbatar da kofar ragon da ta shelanta kan kasar Venezuela inda a jiya Lahadi tana

Gwamnatin shugaban kasar Amurka Donal Trump ta kara karfi wajen tabbatar da kofar ragon da ta shelanta kan kasar Venezuela inda a jiya Lahadi tana kokarin kwace tankar dakon mai na kasar ta Venezuela karu na uku.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa gwamnatin kasar Amurka tana son gurgunta kamfanin hakar man fetur na kasar Venezuela. A ranar 16 ga watan Dicemban da muke ciki ne gwamnatin Trump ta bada sanarwan rufe sararin samaniyar kasar Venezuela da kuma hana dukkan jiragen dakon man fetur fita daga kasar.

Kafin haka shugaban kasar Amurka Donal Trump ya shaalwashin kauda Nicolas madoro daga kan kujerar shugabancin kasar Venezuela.

Jirgin ruwan kasar Venezuela na ukku wanda sojojin Amurka suke son kwacewa dais hi ne mai suna Bella1 jirgin yana karkashin takunkuman Amurka tun shekara ta 2024 saboda huldar da takeda Iran da kuma kungiyar Hizbullah nakasar Lebanon.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted