National Interest:Amurka Ta Saci Jirgin Sama Maras Matuki “Shahid 136” Na Iran Tana Yin Kwafinsa

Marubucin kasidar a cikin mujallar ta “National Intrest” Brandon j. Weichert ya bayyana cewa; rundunar Amurka ta “Marines” sun dukufa wajen kera jirin sama maras

Marubucin kasidar a cikin mujallar ta “National Intrest” Brandon j. Weichert ya bayyana cewa; rundunar Amurka ta “Marines” sun dukufa wajen kera jirin sama maras matuki da su ka bai wa sunan; “Locas” da zai zaman a kai hare-hare ne.

Marubucin ya kara da cewa, wannan jirgin da rundunar ta “Marines” suke kerawa kwafi ne daga jirgin sama maras matuki na Iran samfurin “Shahid 136” da hakan yake a matsayin wani sauyi a tarihin sojojin Amurkan.

Amurka dai tana alfahari da cewa ita ce a gaba wajen kere-keren makamai na zamani, sai dai kuma yanzu tana satar fasahar Iran.

Marubucin ya yi tambaya da cewa, idan kuna cewa Iran kasa ce da ba ta ci gaba ba, to me ya sa a yanzu kuke satar fasaharta?

Haka nan kuma ya ja kunnen masu mulkin Amurka da cewa, abinda suke yin a satar fasahar Iran, da yin kwafinta, ya rusa parpagandar da su ka rika watsawa na cewa, Iran kasa ce da ba ta ci gaba ba.

Wani sashe na kasidar ya yi Ishara da cewa, abinda Amurkan ta yi, yana tabbatar da cewa ta amince da ci gaban da Iran ta samu ta fuskar soja, kuma abu ne mai yiyuwa tana a wasu abuuwan na ci gaba a wannan fagen da a nan gaba za ta shammaci Amurka da su.

Shi dai jirgin “Shahid 136” maras matuki na Iran yana iya yin tafiyar sa’o’I 16 zuwa 20, da nisan kilo mita 4000. Kuma yana dauke da abubuwa masu fashewa da nauyinsu ya kai kilo 50, haka nan  kuma yana da wahalar tsinkayo tafiyarsa a cikin na’urorin Radar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted