A jiya Asabar ne a nan Tehran aka kaddamar da kan sarki na musamman saboda cikar shekaru 1500 da haihuwar manzon Allah ( s.a.) a wani taro na musamman da aka yi da ya sami halartar mataimakin shugaban kas ana farko Muhammad Riza Arif da kuma manyan jami’an gwamnati.
Bugu da kari, bikin ya sami halartar ministoci da malaman addini da kuma masu bakin fada aji a fagen raya al’adu.
Mataimakin shugaban kasar ne ya sa hannu akan babban kan sarki da aka gabatar wanda aka tsara shi bisa salo zane na fitaccen mai fasahar zane na Iran Mahmud Farshijiyan, kuma hukumar gidan waya ta buga shi.
Manufar yin wannan kan sarkin dai shi ne kokarin wanzar da ayyukan fasaha na musulunci da Iran, a matsayin kafar tattaunawa a tsakanin al’adu da kuma isar da sakon da manzon Allah ( s.a.w) ya zo da shi ga bil’adama.
A shekara mai zuwa ne za a yi gagrumin maulundin manzon Allah ( s.a.w) na kasa da kasa a nan Iran domin cikar shekaru 1500 da haihuwarsa.
Bangaren dake kula da sha’anin mata da iyali na ofishin shugaban kasar Iran, ya sanar da cewa; Ofishin shugaban kasar Iran zai shirya taron musamman akan iyali a lokacin cikar shekara 1500 daga haihuwar manzon Allah ( s.a.w) a cikin watan Mayu na 2026.
Sanarwar ta kuma ce taron zai zama dama ce da za yi tattaunawa a tsakanin gwamnatoci, masana da masu fafutuka a fagen zamantakewa daga kasashen duniya mabanbanta.
Daga cikin manufofin taron da akwai bijiro da muhimmanci iyali a rayuwar manzon Allah (s.a.w) da kuma bayyana rawar da zai taka wajen fuskantar kalubalen da ake fuskanta a wannan zamanin a tsarin zamantakewa da rayuwar yau da kullum.