Rahotanni Sun Nuna Cewa HKI Na Gina Sabbin Sansanonin Sojojinta  A Gaza

Hotunan Tauraron dan adam wanda a gaza sun nuna cewa gwamnatin HKI tana gina sabbin sansanonin sojojinta a Gaza tun bayan tsagaita wuta a yankin

Hotunan Tauraron dan adam wanda a gaza sun nuna cewa gwamnatin HKI tana gina sabbin sansanonin sojojinta a Gaza tun bayan tsagaita wuta a yankin a cikin watan Octoban da ya gabata.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin bincike mai suna “Forensic Architeture” na bada sanarwan haka, cibiyar ta kara da cewa Gwamnatin HKI ta kara gina akalla sabbin sansanonin sojojin HK akalla 13 tun bayan tsagaita wuta a ranar 10 ga watan Octoba na wannan shekara mai karewa.

Banda haka labarin ya kara da cewa yahudawan suna kara fadada sansanonin sojojin yahudawan 48 da suke Gaza, wanda yake tabbatar da cewa batun janyewar sojojin daga Gaza, a matsaki na biyu na wannan tsagaita wuta karya ce.

Banda haka a ranar Jumma’a ce Amurka ta jagoranci taro da ministocin harkokin wajen kasashen Masar, Qatar da kuma Turkiyya a birnin Miami na jihar Florida a kasar ta Amurka inda suka tattauna marhala ta gaba na tattauna tsagaita wuta a Gaza, wanda ya hada da shirin kwance damarar dakarun Hamas da kuma samar da sabuwar gwamnati wacce zata gudanar da harkokin Gaza. Kungiyar Hamas dai ta bayyana cewa ba zata mikamakamanta ba matukar ba’a kafa kasar Falasdinu mai cikekken yencin ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted