Hamas Ta Bukaci Taron Miami Ya Kawo Karshen Keta Yarjeniyar Tsagaita Watan Da HKI Ta Ke Yi

Wani babban jami’in kungiyar Hamas a Gaza ya fadawa kamfanin dillancin labaran Afp na kasar Faransa kan cewa dole ne taron Miami na jihar Florida

Wani babban jami’in kungiyar Hamas a Gaza ya fadawa kamfanin dillancin labaran Afp na kasar Faransa kan cewa dole ne taron Miami na jihar Florida wanda aka fara a jiya Jumma’a ya yi maganar keta hurumin  tsagaita wuta wanda HKI take yi tun bayan tsagaiya wuta a cikin watan Octoban da ya gabata.

Shafin yanar gizo na Labarai Arabnews ya bayyana cewa witkoff jakadan Amurka na musamman a gaban ta tsakiya zai gana da wakilan kasashen Qatar, Turkiyya, Masar, a birnin Miami na jihar Florida a kasar Amurka. Kuma ana saran zasu tattauna batun marhala na biyu na tsagaita budewa juna wuta a Gaza yan watanni da suka gabata.

Akwai batun kwance damarar dakarun Hamas, da kuma kawo sojojin kasa da kasa don gudanar da al-amura a Gaza.

Amma hamasa ta ce da farko su takurawa HKI ta bar shiga da fita zuwa gaza ga Falasdinawa, da kuma kwarar kayakin agaji zuwa cikin Gaza kamar yadda aka yi  alkwaki da ita tun farkon tsagaita wutar.

Labarin ya kara da cewa ya zuwa yanzu tun bayan ysagaita wutar sojojin yahudawa sun kasahe 395 . sannan tun lokacin fara yakin kuma an kashe mutane kimani 70.0000.

Sai kuma shugaba kungiyar Khalilul Hayya ya kungiyar Hizbullah ba zata taba aiji makamanta ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted