Jami’an yan sandan birtaniya sun kama wasu masu zanga-zangar nuna goyon bayan falasdinawa guda 11 a lokacin wata zanga zanga a birnin London bayan da jamai’an suka tilasta musu ficewa daga gaban ofishin prime ministan zuwa ma’akatar shari’a bisa umarnin da yan sanda suka bayar da ake cece kuce akai,
Kama wadannan yan gwagwarmaya yana nuna damuwar da ake shi kan yadda ake take yancin furta albarkacin baki a birtaniya, saboda yadda hukumomi ke ci gaba da muzgunawa masu goyon bayan falasdinu karkashin dokar kare hakkin jama’a da kuma yaki da tsattsauran ra’ayi
Zanga zangar ta hada da fitattaun yan siyasa da kungiyoyin fararen hula kuma sun fi mayar da hankali wajen yin tir da matsayin da birtaniya ta dauka kan yakin Isra’ila a Gaza da kuma yin shiru kan yajin kin cin abinci .