A wani jawabin hadin giwa tsakaninsa na tokwaransa na kasar Rasha, Abbar Aragchi ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa, bida a binda ya gabata, tattaunawa tsakanin Iran da Amurka zai yu ne kawai idan Amurka ta sauya halayenta ta dawo kan ra’ayin adalci, dai-daito tsakanin kasashen biyu da mutunta juna ba a matsayin shugaba da mabiyinsa ba, shugaba da bawansa ba.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa Aragchi da Lavrof sun hadu a birnin Mosco a ramar laraban da ta gabata suka tattauna batun bunkasar al-amuran tattalin arziki, kasuwanci, siyasar yankin Asia ta kudu da kuma abubuwan da suke faruwa duniya.
Mosco ta bayyana goyon bayanta ga shirin nukliyar kasar Iran ta zaman lafiya, sannan ta yi watsi da takunkuman tattalin arzikin kasashen yamma, masu tsauri kan kasar Iran.
Ya bayyana bayyana goyon bayansa kan yadda dangantaka tsakanin kasashen biyu yake zurfafa, yake kuma kara karfi a bangarori daban –daban.
Kasashen biyu sun jadda matsayinsu na aiki tare a fagagen diblomasiyya, kasuwanci, sifiri, tsaro da kuma dangantakarsu a cikin kungiyoyi kamar BRICS da MDD da sauran kungiyoyin dasuke cikinsu.