Bangaren dake kula da sha’anin mata da iyali na ofishin shugaban kasar Iran, ya sanar da cewa; Ofishin shugaban kasar Iran zai shirya taron musamman akan iyali a lokacin cikar shekara 1500 daga haihuwar manzon Allah ( s.a.w) a cikin watan Mayu na 2026.
Sanarwar ta kuma ce taron zai zama dama ce da za yi tattaunawa a tsakanin gwamnatoci, masana da masu fafutuka a fagen zamantakewa daga kasashen duniya mabanbanta.
Daga cikin manufofin taron da akwai bijiro da muhimmanci iyali a rayuwar manzon Allah (s.a.w) da kuma bayyana rawar da zai taka wajen fuskantar kalubalen da ake fuskanta a wannan zamanin a tsarin zamantakewa da rayuwar yau da kullum.
Haka nan kuma an tsara taron ne adaidai lokacin mauluncin manzon Allah ( s.a.w) domin ya zama damar bayyana yadda tsarin rayuwar iyali ya kamata ta kasance a karkashin koyarwar musulunci, da kuma jaddada kima da daraja ta bil’adama, da rahama, da adalci, sannan tattaunawa a cikin tsarin rayuwar iyalin.
Haka nan kuma masana da kwararru za su yi musayar ra’ayi akan kwarewar da suke da ita a fagagen siyasa, da bijiro da hanya mafi dacewa da za a karfafa ginshikin rayuwar iyali.
Daga cikin kalubalen da ake son yin musayar ra’ayi akansu a yayin wannan taron, da akwai yadda ginshikin rayuwar iyali ya yi rauni a wannan zamanin, da tasirin hakan a cikin rayuwar zamantakewa, sai kuma batutuwan da su ka shafi hakkokin mata da kananan yara, da yadda salon rayuwa yake sauyawa. Za kuwa a yi hakan bisa la’akari da aiki tare a tsakanin kasashen musulmi da kuma cibiyoyi masu karfin tasiri a duniya.
Mataimakin ministan harkokin wajen Iran mai kula da alakar kasa da kasa, Kazim Garib Abadi, ya gana da babban magatakardar kungiyar kasashen musulmi, Husain Ibrahim Taha, inda su ka tattauna muhimmancin batun iyali a cikin duniyar musulmi da kuma azamar jamhuriyar musulunci ta Iran, wajen shirya wannan taron.
Garibabadi ya yi ishara da aniyar Iran na yin gaggarumin bikin Maulidin manzon Allah ( s.a.w) na cika shekaru 1500 daga haihuwarsa.
A nashi gefen, babban magatakardar kungiyar kasashen musulmin ya jinjinawa rawar da jamhuriyar musulunci take takawa a cikin kungiyar, sannan kuma ya bayyana cikakken goyon bayan kungiyar ga shirin na Iran