Venuzuwela Ta Kai Karar Amurka Gaban Kwamitin Tsaron Na MDD

Ministan harkokin wajen kasar Venuzuwela Ivan gil ya bayyana cewa sun aike da wasikar koke ga kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya wanda a ciki

Ministan harkokin wajen kasar Venuzuwela Ivan gil ya bayyana cewa sun aike da wasikar koke ga kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya wanda a ciki suka yi tir da kwace tankar man venuzuwela da kasar Amurka ta yi,

Babban jami’an na venuzuwela yace kasarsa za ta ci gaba da yin amfani da hakkinta na kare martabar kasar ta hanyar doka har sai ta karfi hakkinat da kuma tallata hajarta,

A ranar laraba da ta gabata ne shugaban kasar Amurka Donald Trump yace dakarunsu sun kwace iko da tankar mai wadda aka ce tana dauke da gangar mai akalla miliyan 200, kuma muna saran zamu rike manfeturdin.

Sai dai gwamnatin karkas ta yi tir da wannan mataki tare da bayyana shi a matsayin babbar sata , ta kuma ci gaba da cewa man fetur da makamashi na alummar venuzuwela ne , kuma ta yi tir da matakin Washington na kwace musu hakkin su da karfin Soja.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted