Yan Bindiga Sun Sace Masu Bauta 13 A Wani Coci A Jihar Kogi Na Tarayyar Najeriya

Akalla mutane 13 yan bindiga suka sace a wani coci a jihar Kogi na tsakiyar tarayyar Najeriya a ranar Lahadin da ta gabata. Shafin yanar

Akalla mutane 13 yan bindiga suka sace a wani coci a jihar Kogi na tsakiyar tarayyar Najeriya a ranar Lahadin da ta gabata.

Shafin yanar gizo na labarai ‘Afircanews’ ya bayyana cewa yan bingidan wadanda ake zaton masu neman kudaden fansa ne, sun bude wuta a cikin cocin kafin su tattara masu bauta 13 su shiga daji da su.

Labarin ya kara da cewa, al-amarin ya auku ne a Cocin Evangelical Church da ke kauyen Aaaaz-kira da ke cikin jihar Kogi a safiyar ranar Lahadi. Kuma kafin haka, kwamishinan watsa labarai na Jihar Kingsley Fanwo ya bayyana cewa an kashe mutane 5 daga cikin wadanda suka kawo harin a yayinda wasu daga cikinsu suka tsere.

Ya ce suna da tabbacin cewa maharan yan bindiga ne masu neman kudaden fansa. Banda haka ya kara da cewa wannan shi ne hari na biyu a cikin makonni biyu da suka gabata, don kafin haka sun kai hari kan Churchin Ejiba inda suka tafi da Pastor guda, da matarsa da kuma mutane 7 da cikin mutanensa, kuma har yanzun suna hannun yan ta’addan.

Kwamishinan ya ce ayyukan Jami’an tsaro a jihohi makwabta a baya bayan nan ne suka koro yan ta’addan zuwa cikinjihar Kogi. Labarin ya kammala cewa duk tare da kokarin gwamnatin tarayyar kasar na dakile ayyukan ta’addanci a kasar har yanzun ana fama da su a jihohin arewa maso yammacin kasar da kuma tsakiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted