Sojojin Isra’ila Sun Harbe Wani Matashi Dan Shekaru 17 A Yammacin Kogin Jodan

Sojojin Isra’ila sun kashe wani matashi bafalasdine a ci gaba da kai hare-hare da suke yi a kudancin gabar yammacin kogin Jodan , kamar yadda

Sojojin Isra’ila sun kashe wani matashi bafalasdine a ci gaba da kai hare-hare da suke yi a kudancin gabar yammacin kogin Jodan , kamar yadda majiyar lafiya ta yankin falasdinu ta bayyana,

Majalisar labarai ta falasdinawa sun bada rahoton cewa sojojin sun harbe matashi ne a kirji a lokacin da suke fito na fito tsakaninsu bayan da sojojin suka mamaye yanki suna ta harbe –harbe da harsashi mai rai, ya ci gaba da cewa an garzaya da matashin mai suna Ammar Yasser Sabah zuwa Asibitin don yi masa magani sai dai daga baya yace ga garinku nan.

Falasdinawa dake zaune a yankin gabar yammacin kogin Jodan sun fuskanci matsaloli masu yawa na  hare-haren isra’ila a yankin da kuma rikici da tsakanin su da yahudawa yan share wuri zauna, alokacin yakin gaza tun daga watan oktoban shekara ta 2023 da ya lakume rayukan mutane 70,000

A watan yulin shekara ta 2024 kotun duniya mai hukumtan manyan laifuka ta bayyana ci gaba da mamayar yankin na falasdinu a matsayin wanda ya sabama doka kuma ta bukaci a kwashe dukkan matsugunan yahudawa dake gabar yammacin kogin Jodan da kuma Gabashin Birnin Qudus,

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted