Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta ce tana da hakkin daukar fansa kan kisan daya daga cikin kwamandojinta wanda ya yi shahada a wani harin Isra’ila.
Babban jami’in Hamas Osama Hamdan ya ce kungiyar tana da hakkin mayar da martani ga keta yarjejeniyar tsagaita wuta da ‘yan Sahayoniya suka yi, musamman kisan kwamandan Raed Saad.
Da yake bayyana hakan ga tashar Al Jazeera, jami’in na Hamas ya Raed Saad a matsayin wanda “ya sadaukar da kansa ga manufar kare Falasdinu.”
Hamdan ya zargi sojojin mamaye da ƙokarin wargaza tattaunawar da ake ci gaba da yi don zuwa mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta.
Ya tabbatar da cewa ana ci gaba da tattaunawa mai zurfi da masu shiga tsakani na yankin, ciki har da Qatar, Masar, da Turkiyya, game da matakai na gaba na yarjejeniyar tsagaita wuta.
Saidai Ya yi gargadin cewa ‘yan mamaya suna haifar da cikas da ba za a iya shawo kansu ba.